<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>197</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Ruhun Allah, Ruhun rai, ka ji addu'armu,
 Ka sauko nan da ikonka, Ruhu mai taimako.

[V2]
 2) Ya Ruhun haske, ga mu nan, mun kira ka yanzu,
 Ka haskaka zukatanmu, ka kori duhunsu.

[V3]
 3) Ya Ruhun wuta, tsarkake harsunan bayinka,
 Har za mu ba da shaidarka da ƙarfin zuciya.

[V4]
 4) Ya Ruhun ƙauna, cika mu da ƙauna cikakkiya,
 Domin mu zama kamarka tun yau har abada.</lyrics>
<title>Ya Ruhun Allah, Ruhun Rai, Ka Ji Addu'armu LW197</title>
</song>